9 Yuli 2021 - 14:01
​Imam Khamenei Ya Isar Da Sakon Ta’aziyar Rasuwar Ahmad Jibril Jigo A Gwagwarmayar Falastinawa

Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya isar da sakon ta’aziyyar rasuwar Ahmad Jibril, babban jigo gwagwarmayar Falastinawa.

ABNA24 : A cikin sakon da Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya isar, ya bayyana Ahmad Jibril a matsayin mutum gwarzo, wanda ya karar da dukkanin rayuwarsa wajen kare hakkokin al’ummarsa, da kuma gwagwarmayar kawo karshen mamayar yahudawan Isra’ila a kan Falastinu.

Jagoran ya ce yana mika sakon ta’aziyar rasuwarsa ga dukkanin al’ummar Falastinu, da kuma dukkanin masu gwagwarmaya da zalunci ‘yan mamaya a Falastinu da ma yankin yammacin Asia baki daya.

Kamar yadda kuma ya mika sakon ta’aziya ga iyalan mamacin, tare da rokon Allah da ya gafarta masa ya kuma lullube shi da rahmarsa.

Ahmad Jibril shi yana daga cikin wadanda suka fara gwagwarmayar kwatar ‘yancin Falastinawa da makami tun a sheakara ta 1959, sanan kuma ya kafa kungiyar kwatar ‘yanci falastinawa ta (Popular Front for the Liberation of Palestine) a cikin shekara ta 1968.

A yammacin ranar Laraba da ta gabata ce Ahmad Jibril ya rasu a wani asibiti da ke birnin Damascus na kasar Syria, bayan fama da rashin lafiya, ya rasu yana da shekaru 83 a duniya.

Shi ma a nasa bangaren shugaba Rauhani ya isar da nasa sakon ta’aziyyar dangane da rasuwar Ahmad Jibril, inda ya bayyana shi ne a matsayin gwarzo wanda tarihin gwagwarmayar Falastinu ba zai taba mantawa da shi ba.

342/